<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>137</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) In ƙyautar Allah ku ke so,
 Ku manya duk da yara ma,
 Yesu shi ne ya shirya ta,
 Yanzu kuwa ta ke samuwa.

[V2]
 KORUS
 Yana so ku ku zo
 Wurinsa, karƃar gafara
 Tun kuna nan a duniya,
 Tun shi ma yana samuwa.
 Yana so ku ku zo
 Wurinsa, karƃar gafara.

[V3]
 2) Ko kuɗi ne bukatarku,
 Sutura ma, ko ci, ko sha,
 Sai da dalili. Shi ya sa:
 &quot;Dalili ya fi dukiya.&quot;
 Korus

[V4]
 3)A wajen ceto haka ma,
 Tafarkin samu, Yesu ne.
 Ko ɗaya ba mai rasawa
 A cikin dukan Masu Bi.
 Korus</lyrics>
<title>In Kyautar Allah Ku Ke So LW137</title>
</song>